Akalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu wasu Kuma suka jikkata yayin da Yan bindiga suka farmaki kauyen Zacholi dake yankin Arewa maso Gabashin kasar Ghana
Kana gidaje da dama ne suka lalace a yankin sanadiyar mummunan hari.
Sai dai Jami’an Yan sanda sun ce, tuni aka fara gudanar da bincike kan faruwar lamarin.
Kazalika haryanzu ba’asan dalilan da suka sanya maharan suka Kai wannan hari ba, Amma hukumomin tsaro a yankin sun ce, dama can yankin na fama da matsalolin tsaro da suka hadar da Fashi da Makami, da kuma rikicin kabilanci.
Harin dai na zuwa ne mako guda bayan Ministan tsaron kasar ta Ghana ya ce, akwai wasu alamu dake nuna yuwuwar Kai wasu hare-haren da ya kira “na ta’addanci.”
Inda kuma ya ce, hakan na da nasaba da yadda ayyukan Mahara ke Kara kazancewa a wasu kasashen dake Makwaftaka da Ghanan.