Wasu da ake zargi mayakan jihadi ne, sun kashe akalla fararen hula 51 a yankin Arewacin Kasar Mali, da sojoji 12 a wani harin kwanton bauna a Burkina Faso da ke makwabtakada kasar.
Wannan ya tayar da hankalin mahukunta kan tsanantar tashe-tashen hankula a kafatanin yankin sahel.
Idan za’a iya tunawa, Maharan dai sun afkawa kauyuka uku, da ke kan iyakar Mali, da Nijar a ranar Lahadi, inda suka kashe dukkan mazauna kauyukan na Karou da Ouatagouna da kuma Daoutegeft.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cutar Tamowa ta addabi Yara a Habasha
Kazalika Maharan sun lalata gidaje bayan dibar ganima na kaya, da shanu da wasu dabbobi. Rahotanni na nunar da cewar, maharan sun zo ne cikin ayari a kan babura dauke da bindigogi.
A wani labarin Kuma.
Taliban: An cire Kasar Afghanistan daga jerin gasar Wasanni ta Tokyo 2020—Inji Jami’ai
A halin yanzu Kasar Afghanistan bazata cigaba da fafatawa a gasar Wasanni ta Tokyo 2020 Paralympics, bayan da Yan Kungiyar masu Jihadi ta Taliban ta karbe iko da Kasar.
Kafin samun nasarar karbe ikon kasar, ana saran yan wasan dambe na taekwondo guda biyu, zasu wakilci kasar a Gasar wasanni ta Paralympics.
“Amma abun damuwa, Kasar Afghanistan bazata cigaba da fafatawa a gasar wasannin ta Tokyo 2020, inji Mai Magana da Yawun Kwamitin wasanni ta Paralympic.
“A dalilin yanayin Al’amurra dake wakana a kasar, an kulle dukkanin filayen Jiragen Sama, to kaga babu wata hanya dazasu bi domin zuwa Tokyo.
“Muna so tawagar Yan wasan da Shuwagabannin su, su kasance suna cikin koshin lafiya a wannan lokaci mai tsanani.”
“Mafarkin yan wasan Afghanistan ne su halarci gasar wasannin Tokyo 2020, amma da wannna lamari, da wuya hakan ta faru”, inji Arian Sadiqi ya bayyana a shafinsu na Twita.
Comments 1