‘Yan sandan Isra’ila sun ce akalla mutane hudu ne suka samu raunuka da safiyar Lahadi, ciki har da biyu masu tsanani, a wani harin bindiga da aka kai a birnin Kudus.
“Wani dan ta’adda dauke da makami irin na Carlo (Bindigu masu sarrafa kansu) sun kai hari a Old City,” in ji ‘yan sanda a cikin wata sanarwa, inda suka kara da cewa, an Farmaki maharin, amma ba tare da bayyana ko an raunata su ba, ko kuma an kashe su.
“Fararen hula biyu sun sami munanan raunuka… sannan wasu ‘yan sanda biyu sun samu raunuka,” in ji ‘yan sandan