Mai Dakin shugaban kasar Amurka Jill Biden ta kai wata ziyarar bazata Kasar Ukraine a yau Lahadi, kamar yadda mai magana da yawunta ya shaidawa manema labarai.
Zuwan nata dai na da nufin ganawa da mai Dakin shugaban kasar Ukraine Olena Zelensky, inda ya ce zasu kuma tattauna kan batun halin da kasar ke ciki da kuma kananan yara da suka rasa matsugunansu sakamakon yakin da ya barke a kasar.
Sanarwa daga jami’an gwamnatin Amurka, ta ce wannan itace ziyara ta farko da suka gudanar a tsakaninsu matan, tun bayan da Rasha ta kaddamar da yaki a kasar Ukraine, ranar 24 ga watan Fabrairu.
Matar shugaban Ukraine ta kuma godewa mai Dakin shugaban Amurka Jill Biden, bisa yadda take aiki Tukuru a ko da yaushe, da kuma karfafa gwiwar mutane.
Kazalika ta sun kuma ziyarci wata makaranta inda wasu yara suke abubuwan kirkire na fasaha ta hanyar amfani da takardar zane domin baiwa iyayen su.
Kazalika suma sun dauki wannan takarda tare da yin abinda yaran ke yi, da nufin karfafa musu gwiwa, wajen ci gaba da aikin da suke wanda yake taimakawa kwakwalwar su da kuma debe musu kewa.
A karshe bayan ta sanar da zuwa ta Rasha, Jill Biden ta kuma ta koma Slovakia.