Mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Abramovich ya sha alwashin sanya makudan kudi don daukar nauyin gangamin yaki da dabi’ar nuna wariya, batun da ke zuwa bayan tarin ‘yan wasan Firimiya ciki har da Marcus Rashford na Manchester United sun fuskanci cin mutunci ta hanyar nuna wariyar a kafafen sada zumunta.
Kalaman na Abramovich na zuwa sa’o’i kalilan bayan Ole Gunnar Solskjaer ya sabunta kiransa wajen ganin kamfanonin da ke kula da kafofin sada zumunta sun mike tsaye wajen yakar dabi’ar ta nuna wariya wadda ke ci gaba da ta’azzara a shafukan.
A cewarsa akwai bukatar hada karfi wajen wayar da kai don kawar da dabi’ar.