Mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Madrid dake ƙasar Andalus ya kamu da cutar nan mai sarƙe numfashi ta Coronavirus da take ci gaba da kama mutane har yanzu.
Rahotanni daga can birnin Madrid na ƙasar ta Andalus ne suka tabbatar da hakan inda shafin ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Athletico Madrid ma sun bayyana hakan a wannan safiya ta Lahadi.
Cutar dai a ‘yan kwanakinnan tana ci gaba da yiwa ‘yan ƙwallo hawan ƙawara yadda ya kamata domin daga kwana 20 zuwa yanzu ta kama ‘yan wasa sama da 40 kuma har yanzu akwai ‘yan wasan da suke da ita kuma ba a gane ba inda wasunsu kuma suke a killace suke karɓar magani.
Diago Simeone dai yana daga cikin gwarazan mai horas wa da duniyar ƙwallon ƙafa bazata manta da suba duba da cewar babu wani mai horas wa mai irin salon da a halin yanzu ganin cewar kowanne mai bibiyar harkokin wasanni yasan wanene shi.
Ayanzu dai ba Semione bane zai ci gaba da jagorantar Athletico Madrid musamman yadda zasu fafata gasar Lalaiga a yau sai dai za a ga mataimakinsa yana jagorantar ‘yan wasan na Athletico Madrid.