Wani matashi daga jiyar Katsina Wanda aka fi sani da MC Tagwaye zai fara haskawa a masanaantar shirya fina finan Hausa wato Kannywood a turance.
Matashi mai suna MC Tagwaye, ya shahara wajen kwaiwayon Shugaban kasa Muhammad Buhari, ta fannin magana da tsarin saka kaya da wadan su dabi’u masu kamanni dana Shugaban.
Wannan dalilin ya saka Jarumin ya sami daukaka a fadin Najeriya da waje, kuma kwaikwayon na Buhari ya bashi damar kusantar Gwamnoni da sauran Mukarraban Jam’iyyar APC har ma ake damawa da shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwato cewar, Wannan shi ne karo na farko da jarumin zai fara Fitowa a wani sabon Shiri a Kannywood mai suna Muqabala, kuma ana kiran shi da suna Ugo, a cikin shirin.
Ana tunanin Sabon shirin Wanda ya tabo bangarori daban daban zai sami daukaka a Idon duniya, jaruma sa suka fito a shirin sun hadar da Jarumi Ali Nuhu da Yakubu Muhammad da Nafisa da dai sauran su.