A yammacin yau Lahadi ne aka yi waje rod da gwarzuwar wasan Tennis din nan na duniya Serena Williams, bayan shan kashi hannun Elena Rybakina.
Rybakina mai shekara 21 ta chasa Williams ne da ci 6-3 da kuma 7-5.
Serena Williams ta taɓa lashe wannan gasa har sau uku a shekara ta 2012 da shekara 2013 da kuma shekara ta 2015.
Yanzu haka wannan rashin nasara ya sa Serena Williams ta zama ta farko a cikin manyan goman farko da ta yi waje rod a gasar.