By Ishaq Dabai
Kakakin Babban Bankin Najeriya CBN, Mista Osita Nwanisobi, ya yi watsi da kiraye kirayen da wasu bangarori ke yi na murabus din Gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele, kan batutuwan da suka shafi farashin canji na Naira.
Mista Nwanisobi ya ce a daren jiya wadanda ke bayan irin wannan kiran suna bin son ransu ne kawai wadanda suka dade suna amfana daga ayyukan neman haya a kasuwar hada hadar kudi ta yau da kullun, wanda yaki amincewa a matsayin wani muhimmin bangare na kasuwar hada hadar kudade ta kasar.
A cewarsa, CBN ba za ta shagala ba a cikin aikinta ta hanyar yin biyayya ga son kai na wasu kalilan don cutar da mafi rinjaye don haka ya bukaci jama’ar bankin da su yi watsi da ikirarin da ake yi na bata sunan Bankin, tare da dagewa cewa Bankin ya ci gaba da himma don aiwatar da aikin da ya wajaba don amfanin jama’ar Najeriya.
Kakakin na CBN ya bada tabbacin cewa babban bankin ya ci gaba da jajircewa don biyan bukatar musayar kasashen waje na matafiya da ke da bukatu na halal dangane da alawus alawus na tafiye tafiye, biyan kudin makaranta, da kudaden magani da dai sauransu.
Mista Nwanisobi wanda ya dage kan cewa babu wani abokin ciniki da ke bukatar canjin kasashen waje don ma’amala ta gaskiya bankunan su za su mayar da su, yana mai kira ga jama’ar bankin da su dage kan hakkokin su da za a ba su muddin sun mallaki dukkan takaddun da ake bukata don tabbatar da bukatar su.
Kakakin ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi taka tsantsan da ayyukan masu hasashe da suka nemi yin magudi a kasuwa saboda dalilai na rashin kishin kasa.