An ruwaito cewa, Basaraken ya rasu ne a wata asibiti dake Abuja Babban birnin tarayya, a yammacin jiya ranar Alhamis.
Wani Saida ya bayyana wa Jaridar Daily Trust cewa, za’a Mai da gawar Mamacin daga Abuja zuwa Masarautar Lifiagi dake karamar hukumar Edu na jihar Kwara a yau juma’a, inda kuma za’ayi Jana’izar shi, kamar yadda addinin Musulunci ya tana da.
Marigayin dai, shi ne sarki Mai darajar ta daya da ya jagoranji yankin tunda ga shekarar 1975, inda ya yi bikin cikarshi shekara 45 a kan karagar Mulkin, a ranar 21 ga watan Octoban shekarar 2020 da ta gabata.
Lokacin da yake tabbatar da rasuwar Basaken, Magatakaddar Masarautar Alhaji Ahmed Kaiama, ya bayyana mutuwar a mastayin babban rashi ga kasar Nupe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje ya zabi Wanda zaigaji Muhuyi Magaji
Kazalika Marigayin shine Shugaban gudanar wa na farko a gidan Rediyon Kwara.
Lokacin da ya ke mika sakon ta’aziyar sa, Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana Marigayin a matsayin Jigo wurin tabbatar da zaman lafiya, da kuma hadin kan Al’uma.
Bugu da kari Gwamnan ya jajantawa daukacin Yan uwa da abokan arzikin na Marigayi Sa’adu Kawu Halirui, da kuma daukacin Masarautar Lafiagi, bisa irin wannan rashi da a kayi.
Inda a karshe ya yi masa fatan Allah ya jikan shi, Ya kuma kyauta makwanci shi.