Shugaban kotun daukaka karan Najeriya, Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa, ta janye daga shari’ar kotun zaben da ke tsakanin shugaba Muhammadu Buhari, da abokin hamayyarsa, Alhaji Atiku Abubakar, a yau Laraba, 22 ga watan Mayu, 2019 a birnin tarayya Abuja.
Hakan ya biyo bayan dogon zaman da akayi yau a kotun zaben kan bukatar da jam’iyyar PDP ta gabatar akan mai Shari’a Bulkachuwa.
Jam’iyyar People’s democratic party PDP ta bukaci Zainab Bulkachuwa ta janye daga karar saboda Uwargida ce ga zababben sanata karkashin jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Lauyan Atiku Abubakar, Livy Ozuokwu, ya mika wannan bukata ne saboda suna tsoron cewa Zainab Bulkachuwa, za ta iya rashin gaskiya a karar.