Yayin da ake ta tsaka da kaulanin wani yunkuri da aka yi na bankare gidan Shugaban Ma’aikatan Shugaban Ibrahim Gambari da zallar karfi, an gano kakakin shugaban kasar Mallam Garbo Shehu ya goge wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita game da wani batu makamancin wannan.
Bai fi Sa’a guda ba bayan da ya wallafa yunkurin fasa gidan Gambari a matsayin kidahumanci da rashin hankali, Garba Shehu ya sake wallafa wani rubutun dake alakanta wata matsala makamanciyar wancan da ta so faruwa a gidan wani jami’i a fadar shugaban kasa wato Abdullahi Maikano.
Wata kafar sadarwa yanar gizo ta wallafa cewa tun daga kan Gambari har mai kano babu wanda ya tsallake fushin yan fashi da makamin domin sai da suka yashe su.
Kamar yadda rahoton ya bayyana wasu yan fashi da makami sun afka gidan mutanen biyu dake Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock inda suka yashe su tass.
Sai daga bisani Mallam Garba Shehu ya yi fatali da wannan rahoto inda ya ce an yi barnar ce kawai a gidan Gambari wanda gidansa kuma ba a Aso Rock yake ba.
Kakakin Shugaban Kasar ya ce an nadi mutanen da suka kutsa gidan a na’urar sirri ta CCTV kuma yan sanda za su yi aikinsu a kan mutanen.
Sai dai daga bisani an ga ya goge rubutun duk da cewa jama’a sama da 200 sun sake wallafawa inda ya sake wallafa sabo wanda babu maganar CCTV cikinsa.
Har yanzu dai ba gano ko cewa Mallam Garba Shehu ya goge rubutun ne saboda dalilai na tsaro da ya ce ana ci gaba da yi ba, don gudun kawo cikas.