An rantsar da sabon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Yakubu Chonoko Maikyau a matsayin shugaban kungiyar na 31.
Daily Trust ta ruwiato cewa, An rantsar da Maikyau ne a wajen rufe taron shekara-shekara na kungiyar karo na 62 da aka gudanar a Eko Hotel, Victoria Island dake Legas a ranar jiya Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: FG Ta Bada Aikin Gadar Da Zai Hada Zangon Kataf Da Karamar Hukumar Kaura
An rantsar da shi ne a gaban dimbin lauyoyin da magajinsa, Mista Olumide Akpata.
Sabon shugaban ya yabawa tsohuwar gwamnatin bisa manyan nasarorin da ta samu a NBA cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ya yi alkawarin ba wai kawai ya ci gaba da samun nasarori da ayyukan da gwamnatin Akpata ta samu ba, har ma da ci gaba da ginawa kungiyar.
A WANI LABARI KUMA: Mutane 2 Sun Mutu, An Ceto 5, Yayin Da Gini Ya Rufta A Abuja
Mazauna garin Kubwa da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shiga cikin firgici bayan da wani bene mai hawa biyu ya ruguje wanda ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da barin ma’aikata da dama amakale.
Ginin wanda ake kan gina shi ya ruguje ne a titin Hamza Abdullahi dake kan titin Gado Nasco