Majalisar dattaɓan Najeriya ta amince da kudi kimanin naira biliyan 74 a matsayin kasafin kudin asusun rundunar yan sandar Najeriya.
Wannan amincewa ta biyo bayan nazari ne da majalisar ta yi kan rahoton hadaka na majalisar wakilai da na dattijai da ya jibacin harkokin yan sanda.
Shugaban kwamitin Sanata Halliru Dauda Jika ya ce lura cewa wannan kasafin kudi shine na biyu tun bayan kaddamar da kudirin Hukumar yan sandar a shekara ta 2019.
Da ma dai hukumar yan sandar ta jima tana jiran wannan rana, inda a yanzu za a iya cewa mafarkin ta ne ya zamo gaskiya.