Kudirin neman shigar majalisar wakilai rikicin da ke tsakanin alkalin alkalan Najeriya Tanko Muhammad da alkalan kotun koli kan batutuwan da suka shafi walwala da kuma yanayin aiki ya fuskanci koma baya a ranar Alhamis.
Yayin da majalisar ta bukaci a sake duba albashi da alawus-alawus na dukkan masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati, majalisar ta shiga wani rudani kan wanda ya kamata su gudanar da aikin.
Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin shari’a, Onofiok Luke, ya gabatar da kudirin neman sa hannun majalisar a rikicin da ya barke a kotun koli da kuma kyautata tsarin jin dadin jami’an shari’a a fadin kotuna.
Luke, wanda ya gabatar da kudirin mai taken, ‘Bukatar a magance tabarbarewar yanayin aiki na jami’an shari’a,’ ya yi fatan majalisar ta bukaci hukumar tattara kudaden shiga da hukumar kasafin kudi da ta sake duba albashin jami’an shari’a daidai da halin da ake ciki na tattalin arziki.
Dan majalisar ya roki majalisar da ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kara wa bangaren shari’a kasafin kudi na shekara mai zuwa tare da samar da kudade na musamman domin bunkasa bangaren shari’a.
Ya kuma roki majalisar da ta baiwa kwamitin shari’a umarnin tabbatar da bin ka’ida tare da bayar da rahoto a cikin makonni shida domin ci gaba da aiwatar da dokar.
A yayin da ‘yan majalisar ke yin gyaran fuska ga kudurorin, mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Wase, ya yi kira da a sake duba tsarin jin dadin duk wasu masu rike da mukaman gwamnati.