Majalisar tarayyar Nijeriya a ranar Laraba a Abuja ta jinjinawa hukumar yaki da rashawa ta Nijeriya wato EFCC bisa nasarar da take samu dangane da yaki da ‘yan damfarar Intanet wadanda suke gurbata tunanin matasa.
Kakakin EFCC din, Wilson Uwujaren a cikin sanarwar da ya fitar ya bayyana cewa; mukaddashin shugaban hukumar EFCC din, Ibrahim Magu shi ne ya tabbatar da hakan a yayin da yake kare kasafin kudin 2020 na naira biliyan 30.92 a gaban ‘yan majalisar.
Ademorin Kuye, memba a kwamitin ya ce hukumar ta taimaka sosai wajen warkar da kasarnan daga cutar cin hanci da rashawa, inda suka haskaka hasken Nijeriya a idon duniya.
Ya jinjinawa EFCC din bisa irin ayyukan da suke gudanarwa.