Rahotannin dake shigowa Dimokuradiya a halin yanzu na nuni da cewa ‘yan majalisar Dattawa da ta wakilai sun shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta janye shirinsa na daukar sabbin ma’aikata dubu dari bakwai da saba’in da hudu (774, 000) a duk fadin kasarnan.
Majalisar ta bayyana hakan ne a zamanta da ta gudanar a jiya Laraba.