Majalisar dokokin jihar Bauchi ta bayyana cewa a shirye ta ke ta fitar da dokar da za ta hana shan taba sigari a jihar.
Jaridar Dimokradiyya ta rawaito cewa Shugaban Majalisar, Abubakar Sulaiman ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a ranar Laraba a Bauchi.
Sulaiman ya bayyana cewa dokar za ta zama wani muhimmin mataki na dakile shan taba sigari, da kuma sanya ido kan masu ta’ammali da ita.
Gwamnan Katsina Ya Halarci Taron Addu’o’i Na Musamman A Kwara
Ya ce maimakon sanya dokar hana shan taba sigari kai tsaye; dokar za ta hana yin amfani da irin waɗannan samfuran.
Sulaiman ya ce ba za a yi la’akari da illolin da ke tattare da shan taba ba saboda masu shan taba ba kadai ba, har ma da wadanda suke a cikin hatsari, wato na kusa da masu shan.
“Abin takaicin shi ne wadanda ke cikin hadarin ba kawai masu shan taba ba ne har da na kusa da su, da ‘yan uwansu, da iyalansu, da makwabta da abokan arziki.
“Yana da mahimmanci mu daidaita shan taba da sauran batutuwan da suka shafi samar da taba da siyar da sigarin.
“Za mu samar da dokokin da za su kare mutanenmu daga illar shan taba,” in ji shi.
Ya kuma jaddada cewa al’umma da ’yan kasuwa da ke harkar noma da sayar da tabar za su fahimci illar abinda suke nomawa ga lafiyar jama’a.
Sulaiman ya ce dokar za ta tabbatar da ingantaccen tsari na kula da samarwa, kera, siyarwa, lakabi, talla, tallatawa da daukar nauyin kayan taba sigarin.
Kakakin majalisar, ya bukaci kungiyoyin farar hula (CSOs) da (CISLAC) da su gaggauta mika daftarin ta’ammali da taba sigarin ga majalisar.