By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dattawa a ranar Laraba, ta tabbatar da nadin mambobin kwamitin kula da harkokin kudi na babban bankin Najeriya (CBN).
DUBA WANNAN LABARIN: Saida Na Halarci Jami’o’i Hudu Kafin Na Kammala Karatu – Mista Macaroni
Tabbatar da wadanda aka nada ya biyo bayan nazarin rahoton da kwamitin kula da harkokin bankuna, inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi suka yi.
Shugaban kwamitin Sanata Uba Sani mai wakiltar (Kaduna ta tsakiya) ne ya gabatar da rahoton.
Shugaba Buhari, a cikin wasikar da ya aike wa shugaban majalisar dattawa,Sanata Ahmad Lawan, kuma mai kwanan ranar 23 ga watan Fabrairu, 2022, ya bayyana cewa an gabatar da bukatar tabbatar da sabunta mambobi da zama mamba ne bisa sashe na 12(4) na dokar babban bankin kasar ta shekarar 2007.
Wadanda Majalisar Dattawa ta tabbatar sun hada da Farfesa Mohammed Adaya Salisu da Dokta Mo’Omamegbe – wadanda dukkansu sabbin mukamai ne.
Sauran mambobi biyar na kwamitin da aka sabunta sun hada da Farfesa Michael Obadan, Farfesa Festus Adeola Adenikinju, Farfesa Aliyu Sanusi Rafindadi, Dakta Robert Asogwa da kuma Alhaji Aliyu Ahmed.
Sanata Sani, a jawabinsa, ya ce wadanda aka zaba sun mallaki cancantar karatu da sanin makamar aiki da gogewar sana’a don zama mambobin kwamitin kula da harkokin kudi na babban bankin Najeriya.