Majalisar dattawa ta amince da sunayen mutane bakwai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mata domin tabbatar da su a matsayin ministoci.
An tabbatar da sunayen mutanen ne bayan an shafe sa’o’i ana tantance su a zauren majalisar dattijai a yau Laraba.
Yayin da aka bukaci wasu daga cikin wadanda aka nada, musamman tsofaffin ‘yan majalisar da su yi bakan-da-baka su fice, wasu kuma an tafka muhawara kan batutuwan da suka shafi kasa.
Idan ba’a manta ba jaridar Dimokuradiya ta ruwaito cewa, Shugaba Buhari, a wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Yunin shekarar 2022, ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da tantance sunayen ministoci bakwai.
Kazalika sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, an gabatar da bukatar tabbatar da sashe na 147(2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 kamar yadda aka yi wa shashin kwaskwarima.
Wadanda aka nada sune: Henry Ikechukwu Ikoh –daga Jihar Abia; Umana Okon Umana – daga Jihar Akwa Ibom; Ekumankama Joseph Nkama- daga Jihar Ebonyi; da Goodluck Nanah Opiah – daga Jihar Imo.
Sauran sun hada da Umar Ibrahim El-Yakub – daga Jihar Kano; Ademola Adewole Adegoroye – daga Jihar Ondo; da Odum Udi – daga Jihar Ribas
A wani labarin kuma na daban.
Za Mu Tura Wakilai Birnin Landan Kan Tsare Ekweremadu Da Matarsa—- Majalissar Dattawa
Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata ta bayyana cewa za ta tura wata tawaga mai karfi domin ganawa da Sanata Ike Ekweremadu a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Idan za’a iya tunawa jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Ike Ekweremadu, wanda shine tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, an tsare shi ne tare da matarsa bisa zargin “cire sassan jiki wani yaro ” a kasar Ingila.
Majalisar ta yanke hukuncin ne bayan sun yi wata ganaawar sirri, na tsawon sa’o’i biyu a ranar Laraba.
Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ahmad Ibrahim Lawan ne ya yabawa lauyoyin da suke kare Sanata Ekweremadu da matarsa, wadanda ya ce suna bakin kokarinsu wajen ganin an fitar da su daga komar rundunar yan sandan birtaniya.
Ya bayyana cewa ya gana da babban kwamishinan Biritaniya wanda ya yi masa bayani kan ci gaban shari’ar da kuma cikakken bayanin abin da ya faru.
Lawan ya kara da cewa tawagar majalisar dattawan za ta hada da mambobin kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje.
“Tawagar majalisar dattawan za ta hada da mambobin kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje wadanda za su yi tafiya nan da kwanaki biyu masu zuwa,” in ji Lawan