By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dattawa, a ranar Talata, ta dage zamanta har zuwa ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu, 2022, kan rasuwar Sanata Ekpenyong Nse Bassey.
Bassey, har zuwa rasuwarsa, shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Oron ta jihar Akwa Ibom a majalisar wakilai.
Babban zauren majalisar ya dage zaman majalisar bayan an dawo daga hutun mako guda daga bikin Easter.
Zaman na ranar Talata ya kasance karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege daga (Delta ta tsakiya).
Dan majalissa Ajayi Boroffice ne ya gabatar da kudirin dage zaman majalisar, sannan kuma shugaban marasa rinjaye, Sanata Philip Aduda ya mara masa baya.
An ruwaito cewa dan majalisar ya rasu ne a ranar Lahadi a Uyo, da karfe 4 na yamma.
Majalisar dattawan, kafin daga bisani ta dage zaman har zuwa ranar Laraba, ta yi shiru na tsawon minti daya domin nuna alhinin rasuwar dan majalisar.
Comments 2