- Majalisar dattawa ta yi watsi da daftarin dokar albarkatun ruwa ta kasa, 2023.
- Hakan ya biyo bayan jera kudurin da akayi don daidaitawa kan takardar odar tare da tantancewa da kuma zartar da shi.
- Kin amincewa da kudirin da majalisar dattawa ta yi ya kawo karshen cece-kucen da gwamnonin da ‘yan majalisar tarayya suka yi.
Majalisar dattijai a ranar Talata ta yi watsi da daftarin dokar albarkatun ruwa ta kasa, 2023.
Hakan ya biyo bayan jera kudurin da akayi don daidaitawa kan takardar odar don tantancewa da kuma zartar da shi.
KARANTA WANNAN: Taleko Ta Koma: Wani Gwamna Ya Dakatar Da Daukar Ma’aikatan Gwamnati
Daily Post ta rawaito cewa kin amincewa da kudirin da majalisar dattawa ta yi ya kawo karshen cece-kucen da gwamnonin da ‘yan majalisar tarayya suka yi, musamman daga kudancin kasar.
A lokacin da aka karanta wannan kudiri a zauren majalisar dattijai, Sanata Gabriel Suswan (PDP Benue ta Arewa maso yamma) ya kafa doka ta 85 na dokokin majalisar dattawa, wanda ya tanadi cewa dole ne Sanatoci su sami cikakkun bayanai na tanade-tanaden duk wani kudirin da zai zo a tare.
Wani dan majalisa, Sanata James Manager (PDP Delta ta kudu), wanda ya goyi bayan Sanata Suswan, ya jaddada bukatar samun cikakkun bayanai kan kudirin tunda an yi tanadin sunan kudirin ne kawai.
Daga baya shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yanke hukuncin amincewa da dakatar da dokar tare da dage zaman majalisar na ranar.
Idan dai za a iya tunawa majalisar ta amince da kudirin ne a shekarar 2020 sakamakon zargin mambobin majalisar da sauran jama’a.
Kafin amincewar shugaban kwamitin kula da albarkatun ruwa na majalisar, Honarabul Sada Soli, ya ce ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya na lokacin Abubakar Malami (SAN) da kwamishinonin shari’a da kuma manyan lauyoyin kasa na jihohi 36. An tuntube su kuma za a sanya ra’ayoyin da aka samu a kan kudirin kuma a rarraba wa dukkan mambobin kungiyar.
A wani labarin kuma,Gwamnan Jigawa Namadi Ya Yi Wasu Sabbin Nade-Nade
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya amince da nadin babban sakataren yada labaran sa.
Sakataren gwamnatin jihar Jigawa Alhaji Bala Ibrahim ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa.
Sabbin nade naden sun fara aiki nan take