Kwamitin majalisar dattijai kan harkokin kiwon lafiya ya koka kan kasafin kudi na 2021 da ministan lafiya, Osagie Ehanire ya gabatar a zauren majalisar dokokin kasa a Abuja ranar Litinin.
Kwamitin ya bayyana takardun da Ministan ya gabatar kan fitar da kudaden a matsayin gazawa kuma wanda bai kammala ba.
Yayin da Ministan a cikin jawabinsa, ya bayyana kudaden da aka samu a kashi 21%, mambobin kwamitin sun ce ya kamata ya fi haka idan aka hada bashin lamuni da tallafi daga abokan hadin gwiwa na kasa duniya.
Musamman, Shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Oloriegbe (APC Kwara ta tsakiya), ya ce bibiyar bayanan da aka tattara yayin ziyarar sa ido a ma’aikatar kudi, babban jari ga ma’aikatar lafiya ya kamata ya zama kusan kashi 62% a karshen watan jiya.
Ya kuma zargi Ministan da kin bayar da rahoton bashin lamuni na Naira biliyan 26 da kuma tallafin da aka samu daga abokan tarayya, wanda duk da haka ministan ya musanta labarin.
Dangane da aiwatar da asusun samar da kiwon lafiya tun daga tushe na shekarar 2018-2021, rahoton kamar yadda ministan ya gabatar ya nuna cewa 45% na zuwa ga cibiyoyin kula da kiwon lafiya mataki na farko, 50% zuwa inshorar lafiya, da 5% ga ayyukan kiwon lafiya na gaggawa, wanda ministan ya ce za a fitar da shi nan ba da dadewa ba a garin Abuja.