Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Mai Shari’a Hussein Baba-Yusuf, don nada shi a matsayin Babban Alkalin Babban Kotun Birnin Tarayya (FCT).
Wannan ya biyo bayan la’akari da amincewa da shawarwarin Kwamitin Majalisar Dattawa kan Shari’a, Hakkin Dan -Adam da Al’amuran Shari’a a zaman taron majalissar a yau Talata.
Shugaban Kwamitin, Sanata Michael Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da rahoton.
Shugaba Muhammdu Buhari a makon da ya gabata ne ya mika sunan Mai Shari’a Baba-Yusuf, domin tantancewa da tabbatar da shi a mukamin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Daliban Makarantar Cocin Katolika a Kaduna
Buhari ya nada Baba-Yusuf a matsayin Alkalin Alkalan Babban Birnin Tarayya Abuja ne tun a ranar 14 ga Agusta, shekarar 2021.
Shugaban ya bayyana cewa, nadin Baba Yusuf a matsayin Babban Alkali na Babban Kotun Abuja ya yi daidai da tanadin Sashe na 256 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nigeria na shekarar 1999.