Majalisar dattawar tarayya ta dakatar da dukkanin zaman daga yanzu har zuwa makonni uku don baiwa yan majalisar dama yin bukukuwar Easter a mazabun su.
Kakakin majalisar Ahmad LAwan shi ya bayyana wannan mataki a yau Laraba yayin rufe zaman majalisar a birnin tarayya Abuja.
Ahmad Lawan ya ce wannan hutu da aka bayar zai kare ne a ranar 13 ga watan Afirelu, to amma ya ce za a ci gaba da tattauna wasu muhimman batutuwa da ya shafi kwamitin majalisar.
Ya kara da cewa ba tare da bata lokaci ba majalisar tana dawo daga hutun na Easter za ta karbi rahoton kwamitin ta kan Kudirin samar da Ma’aikatar Man Fetur da kuma Kuduri kan gyaran fuska wa Dokar Zabe don aiki a kai.