Majalisar Dattawa ta bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta duba yuwuwar barin ‘yan Najeriya da ke daure a gidajen gyaran hali su kada kuri’a a lokacin babban zabe.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Sanata Abba Moro (PDP-Benue) ya gabatar a zauren majalisar na yau Talata.
Da yake gabatar da kudirin, Moro ya ce fursunonin da ake tsare da su ‘yan Najeriya ne da ya kamata a bar su su yi amfani da ‘yancin kada kuri’a da tsarin mulki ya ba su a lokacin zabe.
“Majalisar Dattawa ta lura cewa wasu haƙƙoƙin ɗan adam ba su da iyaka kuma suna zuwa a zahiri tare da haihuwar mutum.
“Daya daga cikin irin wadannan hakkoki shi ne na zama dan kasa, zaman gidan yari duk da cewa yana daya daga cikin dalilan da doka ta tanada na hana mutum ko wanda ya aikata laifin da ake tsare da shi wasu hakkoki, ba za a iya kwace hakkin zama dan kasa a kowane lokaci ba.
‘Yan kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya zo da hakki da kuma hakkokin jama’a da dama, daya daga cikinsu shi ne ‘yancin kada kuri’a a babban zabe.
Don haka Majalisar Dattawa ta bukaci INEC da ta hada kai da Hukumar Gyaran Najeriya don gano wuraren zabe a cibiyoyin da ake tsare da su a fadin kasar nan gabanin babban zaben 2023.