•Majalisar dattijai zatayi tsari Mai kyau, Kan a kasafin kudin Shekara ta 2022.
• Sanata Uba sani ne ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook.
• Majalissun biyu zasu zauna domin tabbatar da komai ya tafi dai dai.
Majalisar dattijan Nageriya ta zauna da ministar kudin Nageriya, a kokarin ta na samar da tsari mai kyau, ga kasafin kudin Shekaru masu zuwa, domin gina ‘yan baya.
Sanata Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya, kuma Shugaban kwamitin inshora, bankuna da sauran harkokin kudi, Malam uba sani ne ya wallafa hotuna a shafinsa na facebook tare da Rubutu Yana Mai Cewa, “A yau ranar Litinin, na shiga cikin tawagar jagorancin Majalisar Dokoki ta Kasa, a wani zama na tattaunawa da Ministar Kudin Nageriya Zainab Shamsuna Ahmed, a kan Tsarin Matsakaitan kudade na 2022 – 2024” inji shi.
Ya ciga ba da cewa, “Tsarin kashe kudade na matsakaici (MTEF) ya fitar da fifikon kashe kudi na matsakaita-lokacin takura wa kan kasafin kudi, wanda yanzu za a iya bunkasawa da kuma tacewa”, a cewar Sanatan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Makarantar shari’a ta saki sakamakon jarabawa na 2021.
Kazalika Sanatan ya ce, “Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban Majalisar Dokoki ta kasa, Sanata Ahmad Lawan ya ce tattaunawar za ta kara zurfafa hadin gwiwar majalisar dokoki, kan hadin gwiwa a cikin kasafin kudi da kuma musamman sassauci ga farkon zartar da Dokar Kasafin Kudin ta shekarar 2022. Hakanan zai tabbatar da cewa, an kiyaye zagaye na kasafin kudin na watan Janairu – Disamba.”
A karshen Sanatan “Yace Wannan ganawa ta kasance ta kasuwanci, da gudanar da shi cikin yanayi na girmama juna da fahimtar juna. Shugabannin majalisar Nageriya za su gabatar da sakamakon tattaunawar ga majalisun biyu, a yayin zama na gaba” Inji Sanatan.