By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu ya ziyarci yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a arewacin kasar.
An kiyasta cewa mutane kusan 850,000 ne yanayin ambaliyar ya shafa a jihar Unity ta kasar.
“Muna tunanin tun da aka sanya hannu kan zaman lafiya, za mu koma cikin lumana idan har an aiwatar da komai, amma da halin da ake ciki yanzu da ambaliyar ruwan ta zo, tuni mutanen dake nan sun karu da yawan mutanen dake fitowa daga sassan kauyukan waje. “Don haka muna da matukar fargaba, bama tunanin zamu bar nan a bana saboda karuwar ambaliyar ruwa”, in ji Beny Makon, mataimakin shugaban sansanin ‘yan gudun hijira na Bentiu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane kusan miliyan 8.3 ne ke bukatar agajin jin kai sakamakon rikici da sauyin yanayi daya haifar.
Nicholas Haysom, Wakilin Musamman na Sakatare-Janar kuma Shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu (UNMISS) ya kara da cewa:
“Ko da muke magana, ruwan na ci gaba da hauhawa, kuma suna cewa a halin yanzu za a kwashe shekaru 15 wajen kau da ruwa, don haka fitar da ruwa ba abu ne da zai dace ba, za mu nemo hanyar da za a baiwa mutane damar yin amfani da shi wajen dawo da rayuwarsu”.
Ambaliyar dai ita ce ta baya-bayan nan ga kasar data fuskanci tashe-tashen hankula tun bayan data samu ‘yancin kai a shekarar 2011.