Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutters ya bukaci da a gaggauta sakin Shugaban Kasar Mali Bah Ndaw da Firaministan kasar Moctar Ouane da sojin Kasar ta Mali suka yi ram da su.
Mutanen biyu su ne ke rike da ragamar kasar bayan wani juyin mulki da sojin kasar suka yi a watan Agusta shekarar da ta gabata, ro amma a jiya sojin kasar suka chafke su tare da tusa keyar su zuwa sansanin soji dake birnin Bamako.
An chafke mutanen biyu ne yan sa’o’i bayan da suka yi wani garanbawul da ya yi sanadiyar tube wasu jami’an soja biyu da suka jagoranci juyin mulkin.
An ruwaito cewa Shi ma dai Ministan tsaron kasar Soulaymane Doucoure na daga cikin mutane da aka yi awun gaba da su da suke tsare hannun sojin.
Manyan Kungiyoyin duniya masu karfin faɗa aji da suka hada da Kungiyar tarayyar Afrika da Kungiyar ECOWAS da EU da kasar Amurka dukkanin su sun yi Allah wadai da matakin kama mutane inda suka bukaci a gaggauta sakin su.