Masana da sauran masu ruwa da tsaki kan harkan ilimi a Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ranar Jumma’a a birnin New York sun koka kan yadda bangaren ilimi yake tabarbarewa, inda suka yi kira ga gwamnatoci daban-daban da su gaggauta kai dauki.
Da suke tattaunawa kan harkar ilimi a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya, sun yi ittifakin cewa, muradun ci gaba, SDGs, ba za a taba cim musu ba idan babu ingantaccen ilimi da kuma tafiya tttare da kowa ba.
Nijeriya ce ta shirya zaman don ranar ilimi ta duniya na shekarar 2020.
A cewar Asusun tallafa wa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, yanzu haka yara kanana da matasa miliyan 258 ne ba sa zuwa makaranta, inda kuma miliyan 617 ba su iya karatu da lissafi ba.
Miliyoyin ‘yan gudun hijira da masu nakasa na daga cikin wadanda ba sa zuwa makarantan, a cewar hukumar.
Shugaban babban zauren Majlisar Dinkin Duniya, Farfesa Tijjani Muhammad-Bande ya ce, alkaluman suna dawo da hannun agogo baya kan nasarorin da aka fara samu a bangaren ilimi.
Muhammad-Bande ya ce, duk da duniya tana ganin yadda ake komawa karatu a kowancce kasa, amma duk da haka da sauran aiki.
Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bayyana irin ra’ayoyin Muhammad-Bande, inda ta ce babu yadda za a yi a cimma muradun ci gaba na SDGs idan aka tafi a kan haka.
A nashi bangaren, mataimakin Shugaban bangaren Majalisar dake bunkasa ilimi, Ambasada Xing Qu, ya jingina matsalar ne ga rashin kayan karatu, rashin kwararrun malamai, rashin isassun gine-gine a makaratu da sauransu.
Shi ma a nashi janibin, Shugaban Education International, Dakta David Edwards, ya koka kan rashin kwarrarun malamai a duk kasashen duniya.
Ya ce, hakan baya rasa nasaba da rashin biyan malamai da kuma rashin kula da ma’aikata a bangaren hukumomin makarantun.