Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci ‘yan bindigar da suka sace daliban makarantar Sakandaren Kankara dake Jihar Katsina da su gaggauta sakin su ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ne ya bukaci hakan ta hannun Kakakinsa Stephane Dujjaric, yayin da ya ke bayyana hari a kan makarantu da cibiyoyin ilimi a matsayin ta ke hakkin Bil Adama.
Guterres wanda ya bayyanawa hukumomin Nijeriya goyan bayansu, ya bukaci jami’an tsaro da su tabbatar da kamo ‘yan bindigar da kumą gurfanar da su a gaban shari’a.