By Abbas Yakubu Yaura
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a jiya Juma’a ya yi maraba da sakin fursunoni da dama da suka hada da manyan ‘yan adawa a kasar Habasha.
Guterres a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su rungumi tattaunawa da sulhu domin samar da dawwamammen zaman lafiya a kasar.
A ranar Juma’a ne kasar Habasha ta saki wasu jagororin adawa da dama daga gidan yari, ta kuma ce za ta fara tattaunawa da ‘yan adawar siyasa bayan shafe watanni 14 ana yaki a lokacin da aka kama dubban mutane.
Yunkurin ‘yantar da shugabanni daga kabilu da dama shi ne nasara mafi girma tun bayan barkewar yaki a arewacin yankin Tigray, wanda ke barazana ga hadin kan kasa ta biyu mafi yawan al’umma a Afirka.
Wasu shugabannin jam’iyyar TPLF, jam’iyyar da ke yaki da gwamnatin tsakiya ta Firaminista Abiy Ahmed, suna daga cikin wadanda aka sako.
Guterres ya yi kira ga bangarorin da su kara kaimi kan wannan muhimmin mataki na karfafa karfin gwiwa ta hanyar amincewa da dakatar da yaki da kuma tsagaita bude wuta mai dorewa, tare da kaddamar da ingantaccen tsarin tattaunawa da sulhu na kasa.
Sannan ya ce, “Zan ci gaba da hada kai da duk masu ruwa da tsaki wajen taimakawa Habasha don ganin ta kawo karshen fadan da kuma maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
“Bayan tuntuɓar da na yi da Firaminista Ahmed, ina kuma sa ran samun ci gaba mai ma’ana a fannin isar da agaji ga duk yankunan da rikicin da aka shafe shekara anayi ya shafa,” in ji shi.
Ya kuma mika sakon fatan alheri ga daukacin ‘yan kasar Habasha masu gudanar da bukukuwan Kirismeti na Orthodox, yana mai addu’ar cewa bikin ya taimaka wajen samun zaman lafiya da wadata a Habasha.