By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma’a ta yi Allah-wadai da “kame” wasu mutane masu zanga-zanga da dama da aka yi a Rasha saboda nuna adawa da mamayar da kasar ta yiwa Ukraine tare da yin kira da a gaggauta sakinsu.
Kakakin ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya Ravina Shamdasani ta shaidawa manema labarai a Geneva cewa, kama mutane da laifin amfani da ‘yancin fadin albarkacin baki ko kuma taron lumana ya zama tauye ‘yanci ba bisa ka’ida ba.
Ta ce hukumar ta fahimci cewa “fiye da masu zanga-zangar 1,800 aka ruwaito an kama su. Babu tabbas ko yanzu an sake wasu.”
Kalaman nata ya zo ne kwana guda bayan da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bijirewa gargadin kasashen yammacin duniya na kaddamar da wani gagarumin farmaki ta kasa da kuma kai hari ta sama kan Ukraine wanda cikin gaggawa ya lakume rayuka da dama tare da raba akalla mutane 100,000 da muhallansu.
An gudanar da zanga-zangar a biranen duniya ciki har da kasar Rasha.
Wani mai sa ido mai zaman kansa ya ce ‘yan sanda sun tsare masu zanga-zangar a birane 51 na Rasha, suna murkushe masu adawa da gwamnati bayan da hukumomi suka gargadi ‘yan kasar kan yin maci.
“Muna kira ga hukumomi da su tabbatar da sakin duk wadanda ake tsare da su ba bisa ka’ida ba,” in ji Shamdasani.
Shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta yi gargadin a ranar Alhamis cewa mamayar na Rasha “a fili ya saba wa dokokin kasa da kasa kuma yana jefa rayukan fararen hula marasa adadi.”
“Dole ne a dakatar da shi nan da nan,” in ji ta.
Ta ce ofishinta zai ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin kuma ta yi gargadin cewa “ana kuma ci gaba da yakin neman bayanai.”
“Yana da matukar mahimmanci a wannan lokacin mu ci gaba da sanya ido sosai tare da ƙoƙarin tabbatar da rahotannin take haƙƙin ɗan adam, gami da hasarar fararen hula, lalata abubuwan farar hula, gami da muhimman ababen more rayuwa, da sauran tasiri kan haƙƙin ɗan adam a ƙasa.”