By Ishaq Dabai
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace ta kwaso gawarwakin bakin haure guda 15 tare da kubutar da 177 daga cikin kwalekwalen masu tsaron teku guda biyu dake komawa Libya wadanda suke kokarin tsallaka tekun Bahar Rum.
Yunkurin tsallakawa daga Arewacin Afirka ya karu a wannan shekara, inda aka bada rahoton cewa bakin haure ko ‘yan gudun hijira sama da 23,000 ne jami’an tsaron gabar tekun Libiya suka yi nasarar kamawa a watan Satumba.
‘Yan ci -rani da ‘yan gudun hijira a Libya na fuskantar tsarewa da cin zarafi, kuma an kama sama da 5,000 a wani farmaki a cikin makon da ya gabata. kuma mutane da dama sun yi nasarar tserewa daga yankin kafin a sake tsare su.
Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Libya tace tana “magance wani lamari mai rikitarwa a cikin fayil na ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, saboda tana wakiltar bala’in ɗan adam da take fuskanta da sakamakon zamantakewar siyasa da shari’a a cikin gida dana duniya”.