By Ishaq Dabai
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, yayi Allah wadai da harin da aka kai kan dakarun wanzar da zaman lafiya a Mali, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani ” kwalkwali ” na Masar guda, da kuma wasu hudu da suka samu munanan raunuka, in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN.
António Guterres ya jajantawa iyalan wanda abin ya rutsa dasu, da kuma Gwamnati da jama’ar Masar, yayin da yayi fatan samun lafiya cikin gaggawa ga sojojin kiyaye zaman lafiya dake aiki tare da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali MINUSMA.
Wani abin fashewa ya fashe a ranar Asabar, inda ya kashe wani sojan kiyaye zaman lafiya na MINUSMA tare da jikkata wasu uku a arewa maso gabashin Mali, in ji wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya.
Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya kuma Shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA, El-Ghassim Wane ya sanar a shafinsa na Twitter cewa motar MINUSMA ce ta bugi wani abu mai fashewa kusa da Tessalit a yankin Kidal.”Adadin wadanda suka mutu daya ne da munanan raunuka guda uku
Babban sakataren ya tunatar da cewa hare haren da aka kai wa dakarun wanzar da zaman lafiya “na iya zama laifukan yaki a karkashin dokar kasa da kasa” sannan ya yi kira ga hukumomin Mali da su “yi kokari wajen gano wadanda suka kai wadannan hare haren domin a gaggauta gurfanar da su a gaban kuliya.
Mali ta kasance wuri mafi hatsari da za a yi aiki a matsayin mai aikin wanzar da zaman lafiya kuma ta fuskanci juyin mulkin soji sau biyu a cikin shekarar data gabata, yanayin tsaro ya tabarbare gaba daya, inda hukumomin gwamnati suka yi rauni.
Babban jami’in na MINUSMA yace “farmakin na matsoraci ne” zai kara karfafa niyyar “himmar tallafawa Mali da mutanenta, a kokarinsu na neman zaman lafiya da kwanciyar hankali.”