Majalisar wakilan ƙasar nan ta fara tattaunawa domin yin gyara da kuma kwaskwarima domin bawa ma’aikatan gwamnati damar gudanar da wasu kasuwanci baya ga noma kamar yadda dokar CCB ta tanadar.
Wannan ƙuduri ya fito ne daga wajen ɗan majalisar dokoki mai wakiltar Andoni/Opobo/Nkoro ta jihar Ribas Awaji-Inombek Abiante.
https://dimokuradiyya.com.ng/majalisar-dattawa-ta-musanta-zargin-ƙarɓar-cin-hanci-daga-hukumar-nddc/
Ɗan majalisar ya ƙara da cewa wannan rashin adalci ne ace wata doka ta hana ma’aikata yin wani kasuwanci sai dai noma.
Har wa yau, yace dole ne a yiwa dokar gyara domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan.
Ya zuwa yanzu dai majalisar zartarwar na duba yiwuwar yiwa dokar gyara dan ganin an fita daga halin matsi da ake ciki a ƙasar nan.