Daga: Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Anambra a ranar Juma’a, ta amince da sake fasalin kasafin kudin shekarar 2022 na Naira biliyan 169.6 zuwa doka kwanaki 55 bayan da gwamna Chukwuma Soludo ya gabatar mata da shi.
Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kasafin kudi na majalisar wanda ya nuna cewa an samar da Naira biliyan 108 don kashe manyan kudade da kuma kashe naira biliyan 61.3 na yau da kullum.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/bayan-mun-garkame-kan-iyakoki-yanzu-haka-yan-najeriya-suna-cin-shinkafar-gida-buhari/
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dokokin jihar Anambra Hon. Obinna Emeneka, wanda ya gabatar da rahoton, ya ce sun yanke shawarar ci gaba da rike girman kasafin kudin da aka yi wa kwaskwarima bayan yin dogon nazari, duk da cewa ba a yi gyare-gyare a wasu ma’aikatu da hukumomi ba.
Shugaban majalisar, Mista Uche Okafor ya yabawa kwamitin bisa yadda ya yi dogon nazari sosai kan kasafin kufin tare da gudanar da kuri’ar amincewa da rahotan.
Okafor ya kuma umurci mukaddashin magatakardar majalisar, Misis Esther Anaetoh, da ta aika da kwafin kudirin ga gwamna Soludo domin amincewar sa.
Har ila yau, a zauren taron, shugaban majalisar ya karanta wata wasika daga Gwamna Soludo, mai kwanan wata 5 ga watan Yuli, inda ya bukaci a amincewa da a ba da lamuni na Naira Biliyan 100 ga Global Limit Multiple Term Facility don ginawa da kuma gyara wasu muhimman ababen more rayuwa a jihar.
An mika wasikar ga kwamitin majalisar mai kula da asusun gwamnati domin tantancewa kuma za su gabatar da rahoto ga majalisar a ranar Alhamis 21 ga watan Yuli.