By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Binuwai ta yi wa dokar hana kiwo a fili ta jihar Benue gyaran fuska ta shekarar 2017, inda ta tanadi hukunci mai tsauri ga masu aikata laifi.
Yanzu dai dokar ta tanadi daurin shekaru 14 a gidan yari tare da zabin biyan tarar Naira miliyan 5 ga duk yara masu matsakaitan shekarun wanda aka kama da laifin kiwo a kowane yanki na jihar.
Gyaran dokar dai an yi shi ne a yayin zaman majalisar biyo bayan nazarin rahoton zaunannen kwamitin kula da harkokin noma da albarkatun kasa na majalisar.
Da yake jagorantar muhawara kan rahoton, shugaban kwamitin kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Makurdi ta Kudu, Mista Terwase Aondoakaa, ya ce gyaran ya yi matukar dacewa don magance wasu kura-kurai da aka samu a farkon dokar.
Sannan ya bayyana cewa dokar da aka yi wa kwaskwarima za ta tanadi tarar Naira 500,000 ga duk wanda aka kama yana safarar dabbobi da kafa a jihar.
Ya bayyana cewa wanda ya sake aikata laifin a karo na biyu za aci tarar sa naira miliyan 1 tare da zaman gidan yari da ya dace, yana mai jaddada cewa, “Sabuwar dokar ta tanadi tarar dabbobi daban-daban da suka hada da tarar naira 50,000 akan kowace saniya,da naira 10,000 kan ko wane alade, sannan da naira 5,000. kan kowacce akuya da kuma kaji kan naira 1,000.”
Ya kuma roki majalisar da ta amince da kudirin dokar da aka gyara domin hana kiwo a fadin jihar da rashin bin doka da oda da kuma rashin mutunta dokar shekarar 2017.
Bayan tattaunawa kan rahoton, shugaban majalisar, Mista Titus Uba ya gayyaci magatakardar majalisar domin ya karanta kudirin a karo na uku bayan haka majalisar ta amince da kudirin ya zama doka.