By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta kafa harabar kwalejin fasaha ta jiha a karamar hukumar Rogo.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na bukatun jama’a da Alhaji Magaji Zarewa, ya gabatar a zauren majalisar, wanda kakakin majalisar Hamisu Ibrahim-Chidari ya jagoranta a ranar Litinin.
Da yake gabatar da kudirin, Zarewa ya bayyana cewa, idan aka kafa harabar makarantar, za ta bunkasa harkar ilimi ga al’ummar yankin, jihar da ma kasa baki daya.
Dan majalisar ya jaddada cewa hakan zai kuma kara habaka tattalin arzikin yankin tare da samar da ayyukan yi ga matasan yankin.
Sannan yace ” Idan aka amince da bukatar za ta rage munanan dabi’u a tsakanin matasa saboda mazauna yankin za su fuskanci yadda kalubalen ilimi yake,” in ji shi.
Zarewa ya ci gaba da cewa ilimi shi ne kadara daya tilo da za’a iya gadarwa matasa masu zuwa.
A nasa bangaren mataimakin shugaban majalisar Alhaji Hamza Massu ya ce idan aka kafa makarantar za ta magance matsalolin da dubban matasa masu neman ilimi ke fuskanta yayi shiga manyan makarantu.
Kabiru Dashi ya kara da cewa Kwalejin zata samar da ayyukan yi ga al’ummar Kiru, Bebeji, Karaye da kuma mutanen da suka fito daga makwabciyar jihar Kaduna.
Bayan zaman da ‘yan majalisar suka yi, majalisar ta amince da kudurin tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta dauki matakin da ya dace kan lamarin.