By Abbas Yakubu Yaura
A yayin da yake bada tasa gudunmawar, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar Legas Setonji David, ya bayyana cewa ciyo bashi yana da adadin riba mai lamba daya tare da tsawon shekaru 30 na loakcin biya.
Ya ce aikin da ake nema na ciyo bashi zai samar da ci gaban tattalin arziki da ci gaba mai dorewa a jihar.
Kakakin majalisar Obasa, bayan da ‘yan majalisar suka kada kuri’ar amincewa da kudurin ciyo bashin ya umarci mukaddashin magatakardar majalisar, Mista Olalekan Onafeko, da ya aika kwafin amincewar mai tsafta ga Gwamnan.
A halin da ake ciki, shugaban majalisar Obasa ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai albarka da Allah ke kaunarsu a cikin wani sako da ofishin yada labaransa ya fitar domin tunawa da bikin Kirsimeti na wannan shekara 2021.
Sannan ya kara da cewa “Dukkan dokokin da Allah ya ba wa mutum za a iya taƙaita su a kan bukatar mu ƙaunace shi da ƙaunar maƙwabtanmu.
“Saboda haka, babu wani ra’ayi cewa idan muka ci gaba da ƙudirinmu, ɗaiɗaiku da kuma gaba ɗaya, mu ƙaunaci juna kamar yadda Yesu ya jaddada, duniya za ta zama wuri mafi kyau,” in ji Kakakin.