A yau Laraba Majalisar dokokin jihar Kaduna ta tsige shugaban masu rinjaye, Alhaji Mohammed Inuwa, mai wakiltar mazabar Doka da Gabasawa.
Hukuncin ya biyo bayan amincewar da mambobin majalisar suka yi na rashin amince wa da shi.
Rahotanni sun nuna cewa, mambobin jam’iyyar APC Mai Mulki guda 17 sun sanya hannu kan wasikar tsigewar Shugaban Masu rinjayen.
Kamfanin Dillancin Labaran Nigeria NAN ya ruwaito cewa, majalissar ta kunshi mambobi guda 34.
KARANTA WANNAN LABARIN: Taliban ta Magantu kan bullar IS a Afghanistan
A nashi bangaren, Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman Majalissar, Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar dokokin jihar Kaduna, Mista Tanimu Musa ya ce, an dauki matakin ne bayan kada kuri’ar yankan kauna kan Shugaban masu rinjayen na majalissar .
“Don haka, an tsige Mabo daga mukamin shi, kuma nan ba da jimawa ba majalissar za ta sanar da sabon Shugaban masu rinjaye” inji shi.
A wani labarin Kuma
Kungiyar Taliban ta mayar da martani kan ikirarin mayakan da ke da alaka da kungiyar IS, kan zargin da ake cewa, IS ta mamaye lardin Kunduz na kasar Afghanistan.
Hajji Najibullah Haron, babban jami’in leken asirin kungiyar Taliban ya ce, IS ba ta mamaye lardin Kunduz na arewacin Afghanistan ba.
Kamfanin Dillancin Labaran Nigeria NAN, ya ruwaito cewa,Haron ya bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe da balantana makama.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar yau Laraba, ya ce: “Zaman lafiya na din-din-din ya dawo lardin Kunduz kuma mutane na zaune cikin kwanciyar hankali a can, kanazalika duk wani rahoto game da kasancewar yan ta’addar IS a Kunduz ba gaskiya bane.” a cewar shi.
Ya jaddada cewa sabuwar gwamnatin Afganistan, ba za ta bari kowa ya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro a Kunduz, ko wani yanki na kasar ba.
Kwanan nan kungiyar Taliban ta karbe ikon gwamnatin Afghanistan bayan ta karbe ikon Kabul Babban birnin kasar.
Comments 1