Majalisar dokokin jihar Kano ta dage ranar da ta sanya tun da fari, domin komawa daga hutun da ta tafi, zuwa wata ranar ta daban.
Duk da cewa sanarwar da Majalisar ta fitar bata bayyana dalilin dage komawar ta ba, amma dai dagewar na zuwa bayan da siyasar Jihar Kano ke ci gaba da daukar zafi.
A bangaren yan majalisar kuwa suma ba a bar su a baya ba, domin kuwa sai rububin ficewa suke daga jam’iyyar su, zuwa wata jam’iyyar ta daban.
Uba Abdullahi shine sakataren yada labaran majalisar, a wata Sanarwa da ya aikowa da Dimokuraɗiyya ya bayyana cewa majalisar zata koma ci gaba da zama ne ranar Litinin 6 ga watan Yuni, 2022.
A cewar Uba Abdullahi wannan mataki na zuwa ne bayan da shugaban majalisar Hamisu Chidari ya bayar da umarnin hakan.
Yanzu dai majalisar dokokin Kano zata ci gaba da kasancewa a Rufe har zuwa ranar da aka ambata a sama domin ci gaba da ayyukan dake gaban ta.