Majalisar dokokin Kano ta kafa kwamiti da zai binciki ambaliyar ruwa da rugujewar gidaje da ake samu a wasu daga cikin kasuwanni da yankunan jihar baki daya.
Majalisar karkashin shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ta kafa kwamitin na musamman da zai duba hakan, a yayin zamanta na Litinin din nan.
Tunda fari dai dan majalisa mai wakiltar Fagge Muhammad Tukur, ne ya gabatar da gudurin gaggawa dake neman majalisar tayi bincike kan musababin ambaliyar ruwan da aka samu a kasuwar Kantin Kwari, dama sauran sassan dake fuskanta a damunar bana tare da tallafawa wadanda iftila’in ya shafa.
KARANTA ANAN: Ku Taimaka Mana Wajen Ganin Mun Kama Mr 442 Da Safara’u – Afakallah
Sai dai bayan tattaunawa da akayi majalisa ta amince kudurin ya hada da sauran kasuwanni da guraren da ambaliyar ruwan ta shafa a ciki da wajen kananan hukumomin jihar nan.
Tuni dai majalisar ta baiwa shugaban kwamitin bada agajin gaggawa na majalisar Aminu Sa’ad Ungoggo, jagorancin kwamitin ayyuka dana muhalli tare da gabatar da rahoton su nan da makwanni biyu domin daukar mataki akai.
DUBA WANNAN 👇👇👇👇
CAN, Babban Limami Sunyi Allah-Wadai da kisan Sheik Goni Aisami