By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin kasar Ghana a ranar Juma’a ta yi watsi da kudirin kasafin kudin shekarar 2022 da gwamnati ta gabatar saboda damuwar da ake yi kan sabon harajin banki na lantarki.
Wannan dai shi ne karon farko da majalissar ta ki amincewa da kasafin kudin kasar tun daga shekarar 1981 a kasar dake yammacin Afirka.
Majalisar dokokin Ghana ta rabu tsakanin manyan jam’iyyun biyu bayan zaben shekara guda da ta gabata, wanda ke kara fuskantar barazanar kaka-nika-yi a yayin da kasar ke fafutukar farfado da tasirin annobar duniya da kuma dimbin basussuka.
Wannan koma baya na ranar Juma’a ya zo ne bayan da gwamnati ta gabatar da wani sabon kuduri na haraji kan hada-hadar bankunan lantarki, gami da shahararrun manhajojin wayar salula.
‘Yan majalisar sabuwar jam’iyyar Patriotic mai mulki sun fice ne bayan sun zargi kakakin majalisar da nuna son zuciya saboda a cewarsa bai kamata ministar kudi ta kasance a yayin kada kuri’a ba.Daga nan ne ‘yan majalisar adawa suka yi watsi da shawarar.
“Majalisa ta ki amincewa da kasafin kudin shekarar 2022,” wanda dan majalisar adawa Sam George ya rubuta a cikin shafinsa na Tweeter. “Mu a matsayinmu na ‘yan tsiraru mun dauki matsaya tare da mutanen Ghana don kin amincewa da kasafin kudin da ke da mugunyar E-Levy, karin kudaden gwamnati da caji. Nasara ga Ghana.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A watan Janairu ne dai aka tilastawa sojoji shiga cikin majalisar dokokin Ghana domin tarwatsa fada tsakanin ‘yan majalisar dake adawa da sakamakon zaben.
Yanzu dai dole ne jam’iyya mai mulki ta shugaba Nana Akufo-Addo ta tattauna da jam’iyyar adawa a majalisar dokokin kasar domin cimma matsaya kan kudirin kasafin kudin.
Ana dai kallon Ghana a matsayin kasar dimokuradiyya mai kwanciyar hankali a yammacin Afirka mai cike da rudani, ko da yake zabukan shekarar 2021 na fuskantar zarge-zargen da ‘yan adawa suka yi nayin magudi, yayin da mutane biyar suka mutu a tashin hankali.