Majalisar dokokin jihar Kano ta fara muhawara kan bukatar samar da karin masarautu hudu a jihar, inda kudurin ya tsallake muhawara ta farko a yau Talata, kudurin wanda zai yi garambawul ga dokokin kananan hukumomi, don samun damar daga darajar wasu masarautu zuwa daraja ta daya. Majalisar ta amince da rahoton kwamitin hadin gwiwa na kananan hukumomi da al’amurran masarautu, da na bangaren shari’a da kuma wanda ‘yan majalisar su ka fitar a daidaikun su, suka fitar kan wannan batun na yi wa dokar garambawul. Majalisar ta fara muhawara kan yi wa dokar kwaskwarima ne bayan da wata camba mai suna Ibrahim Salisu Chambers, suka shigarwa da majalisar korafin neman a kara yawan masarautu hudu da sarakuna masu matsayin daraja ta daya, a masarautun Karaye, Bichi, Rano da Gaya. Korafin ya bayyana cewa kara yawan masarautun masu daraja ta daya za su kara samar da ci gaba a jihar Kano, sannan za su kara samar da alaka mai karfi tsakanin masarautun da gwamnatin jihar Kano, za a samu karin tsaro da ci gaban kasa. A daidai lokacin da shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Baffa Danagundi ya bayyana cewa rahoton ya bada shawarar samar da karun masarautun hudu, bayan da aka yi zaman shawara da masu ruwa da tsakin a jihar Kano din. Tsohon gwamnan jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi ya samar da karin masarautu a shekarar 1982, daga baya magajin shi marigayi Sabo Bakin-Zuwo ya rushe masarautun, jihar Kanon ta na da Sarkin daya ne kacal, a yanzu Sarkin Kano shine Muhammadu Sanusi na biyu, sai hakimai a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.