A ranar Litinin ne majalisar dokokin jihar Kano ta tantance sabbin kwamishinoni guda tara da gwamna Abdullahi Ganduje ya nada.
Kakakin majalisar, Hamisu Ibrahim-Chidari ne ya sanar da karbar wasikar da Ganduje ya aika wa Majalissar na karin wanj kwamishina guda mai suna Aminu Ibrahim-Tsanyawa. Kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito
A ranar 15 ga watan Agusta ne Ibrahim-Chidari ya karanta wasikar farko daga gwamnan.
Nade naden ya biyo bayan murabus din da wasu ‘yan majalisar zartaswar jihar suka yi na tsayawa takara a shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Na Fita Daga NNPP — Shekarau Ya Zargi Kwankwaso Da Wulakantashi
Kwamishinonin su ne Ibrahim Dan’azumi, Abdulhalim Abdullahi, Lamin Sani-Zawiyya,Ya’u Abdullahi-Yan’shana.
Sauran sun hada da Garba Yusuf Abubakar, Yusuf Jibirin, Adamu Fanda, Saleh Kausami, da Ali Burum-Burum.
An tabbatar da su ne bayan da ‘yan majalisar suka tattauna kan Sunayen wadanda suka yi nasarorin da suka samu.
Daga bisani aika da wasikar gayyata ga Ibrahim-Tsanyawa da ya bayyana a gabar majalissar ranar Talata domin tantancewa.
A WANI LABARIN KUMA: Atiku Ya Sha Alwashin Mika Jami’o’in Tarayya Ga Gwamnatin Jihohi Idan Aka Zabe Shi A 2023
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin mika jami’o’in gwamnatin tarayya ga gwamnatocin jihohi idan aka zabe shi a shekarar 2023.
Da yake jawabi a wajen bude taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya a Legas, Atiku ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta da albarkatun da ba su da iyaka, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Masha Allah