Majalisar jihar Kano ta tantance tare da tabbatar da mutum 20 da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tura gaban majalisar domin tabatar da su a matsayin Kwamishinoni.
Kakakin Majalisar, Alhaji Abdulazeez Garba-Gafasa shi ne ya jagoranci shirin tantancewar wanda aka kwashe awanni uku ana yi kafin tabbatar da mutum 20 din a matsayin Kwamishinonin Ganduje.
Rahotanni sun bayyana cewa wadansu daga cikin Kwamishinonin sun taba zama ‘yan majalisa, a yayin da wasun su Kwamishinoni ne a wa’adin farko. Inda wannan ya sanya wadansu mintoci kawai suka dauka aka tabbatar da su.
A ranar Litinin ne, Kakakin majalisar, ya karanta sunayen mutum 20 da gwamna Ganduje ya aikawa majalisar domin tantance su a matsayin Kwamishinoni.
Daga cikin Kwamishinonin da a sun rike mukaman a wa’adin
farko akwai Kwamishinan yada labarai, Muhammed Garba, da na lura da kananan
hukumomiAlhaji Murtala Sule-Garo.
Sauran sun hada Ibrahim
Mukhtar, Musa Iliyasu-Kwankwaso, Kabiru Ibrahim-Getso, Shehu Na’Allah-Kura,
Mukhtar Ishak-Yakasai and Muhammed Tahir-Adam.
Sabbin Kwamishinonin da aka nada sun hada da; Ma’azu Magaji, Nura Muhammad-Dankade, Zahra’u Umar-Muhammad, Aminu Ibrahim-Tsanyawa, Sadiq Aminu-Wali, Muhammad Baffa-Takai da Kabiru Ado-Lakwaya.
Sai kuma Mariya Mahmoud-Bunkure, Ibrahim Ahmad-Karaye,
Mahmoud Muhammad-Dansantsi, Muhammad Sanusi-Sa’id da Lawan Abdullahi-Musa.