By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar matasan Najeriya reshen jihar Kogi, ta yi Allah wadai da hauhawar farashin buhun ruwan leda a jihar wanda ya tashi daga N10 zuwa N20.
A cikin wata sanarwa da shugaban NYCN na jihar Usman Samuel Ogohi ya fitar, majalisar ta ce tana ganin karin farashin da kungiyar masu samar da ruwan tsafta ke yi a matsayin wani mummunan yunkuri na ganin ba za a iya jurewa rayuwar al’ummar jihar ba. Ya yi alkawarin yin tsayin daka kan canjin farashin kayayyakin.
Ogohi ya karyata ikirarin da kungiyar ta yi na cewa tsadar kayan masarufi ne ya janyo tashin farashin buhun ruwan leda wato (pure water). Ya bayyana cewa farashin ruwan leda a wasu jihohin bai canza ba.
“Muna da kyakkyawar fahimta ta hanyoyin sadarwar mu a wasu jihohi cewa farashin kayan, galibin kayan da ake bukata wajen samar da tsaftar ruwa ya tsaya cak a cikin watanni takwas da suka gabata.
“Farashin buhunan ruwan leda a jahohi kamar su Benue, Edo, Ondo, Ekiti da ma Neja ya ci gaba da wanzuwa,” in ji shi.
Shugaban hukumar na jihar ya kuma tabbatar da cewa NYCN na sane da matakin da kungiyar ta dauka na haifar da karancin kayan masarufi domin kara yawan bukatu da kuma ba da damar tashin farashinsu ya tsaya.