By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta tantance tare da tabbatar da wata lauya mai suna Hannatu Abimiku mai shekaru 28 da kuma wasu kwamishinoni 14 wanda gwamnan jihar Abdullahi Sule ya aika mata.
A ranar Alhamis din data gabata ne Sule ya gabatar da sunan matashiyar mai shekaru 28 data kammala karatun aikin lauya wanda ta fito daga karamar hukumar Lafiya ta jihar tare da wasu mutane 14 da majalisar dokokin jihar zata tantance kuma ta tabbatar dasu.
Da yake bayyana hakan a zaman da majalisar ta yi a Lafiya a ranar Laraba bayan kammala aikin tantancewar, Kakakin Majalisar, Ibrahim Abdullahi, ya bukaci wadanda aka nada na kwamishinoni dasu yi aiki tukuru yayin da suke gudanar da ayyukansu a lokacin da Gwamna ya rantsar da su.
Ya ce, “Ina mai farin cikin sanar da cewa, bayan kammala tantance kwamishinoni 15 da Gwamna Abdullahi Sule ya aiko mana dasu, ‘yan majalisar ne suka tabbatar dasu. Don haka za mu jira ranar bikin rantsar dasu.
“Wadanda aka tabbatar sun hada da Yakubu Kwanta daga karamar hukumar Akwanga, Hannatu Abimiku daga karamar hukumar Lafiya, Yusuf Turaki daga karamar hukumar Awe, Aishatu Ibrahim daga karamar hukumar Awe, Salihu Enah daga karamar hukumar Doma, Umar Gurku daga karamar hukumar Karu, Nuhu Oshafu daga karamar hukumar Keana, Idris Mohammed. -Idris daga karamar hukumar Keffi da Abdulkareem Kana daga karamar hukumar Kokona.
“Sauran sun hada da Mohammed Sarki daga karamar hukumar Lafia, Fatu Sabo daga karamar hukumar Nasarawa, Yakubu Lawal daga karamar hukumar Nassarawa Eggon, Daniel Agyeno daga karamar hukumar Obi, Ahmed Baba-Yahaya daga karamar hukumar Toto da Lucky Yargwa daga karamar hukumar Wamba,” a cewa sa.
Shugaban majalisar ya umurci magatakardar majalisar daya sanar da kudurin majalisar ga Sule domin ci gaba da daukar mataki.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Tun da farko, shugaban masu rinjaye na majalisar, Tanko Tunga, mai wakiltar mazabar Awe ta Arewa, ya gabatar da kudirin tabbatar da sunayen kwamishinoni yayin da shugaban marasa rinjaye, Abel Bala mai wakiltar Nasarawa Eggon ta Yamma ya goyi bayan kudirin.