Majalisar dokokin jihar Oyo ta amince da nadin Bayo Lawal a matsayin mataimakin gwamnan jihar.
‘Yan majalisar dokokin jihar sun amince da hakan ne da yammacin ranar Litinin din nan bayan tsige Rauf Olaniyan a matsayin mataimakin gwamnan jihar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa ‘Yan majalisar dai sun tsige Olaniyan ne bisa zargin rashin da’a.
An cimma matsayar tsige shi ne bayan da ‘yan majalisar suka gabatar da kuma duba shawarwarin kwamitin mutum bakwai da babban alkalin kotun, Munta Abimbola ya kafa domin bincikensa kan zarge-zargen da ake masa na rashin da’a da kuma cin zarafin ofishinsa.
Tsigewar bisa ga majalisar ya fara aiki nan take.
A cewar rahoton kwamitin da shugaban masu rinjaye na majalisar Hon Sanjo Adedoyin ya gabatar a zaman majalisar na ranar Litinin, kwamitin mai mutane bakwai ya samu mataimakin gwamnan da dukkan zarge-zargen da ake masa.
Dukkan ‘yan majalisar wakilai 23 na jam’iyyar PDP a zauren majalisar sun kada kuri’ar amincewa da shawarwarin kwamitin.
An kafa kwamitin binciken ne a makon da ya gabata don gudanar da bincike a kalla zarge-zarge biyar da ke kunshe a cikin karar da aka shigar kan Olaniyan.
An zabi Olaniyan a matsayin gwamna a shekarar 2019 tare da Gwamna Seyi Makinde a karkashin jam’iyyar PDP amma sai ya samu sabani da gwamnan na tsawon lokaci.
A yanzu, bambance-bambancen da ke tsakanin mutanen biyu da alakar aikinsu ya tabarbare kuma ya zama ba a daidaita ba a lokacin da Mataimakin Gwamnan ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar APC.